logo

HAUSA

An samu gawarwaki biyu daga ginin da ya rushe a kudancin Nijeriya

2022-09-04 19:56:06 CMG Hausa

 

Gawarwaki akalla 2 aka gano daga burbushin wani gini mai hawa 7 da ake aikin gininsa a Lagos, cibiyar hada-hadar tattalin arziki ta Nijeriya da sanyin safiyar yau Lahadi.

Shugaban hukumar kula da agajin gaggawa ta Nijeriya a shiyyar kudu maso yammacin kasar, Ibrahim Farinloye, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami’an hukumomin aikin ceto dake ayyukan bincike da ceto ne suka gano gawarwakin.

Ya ce mutane akalla 6 ne suka makale a lokacin da ginin dake kan titin Oba Idowu Oniru na birnin Lagos ya rushe da misalin karfe 3 na sanyin safiyar yau Lahadi.

Jami’in ya kara da cewa, ba a san musababbin rushewar ginin ba, amma an kaddamar da bincike. (Fa’iza Mustapha)