logo

HAUSA

Kamfanin Gazprom na kasar Rasha ya dakatar da tura iskar gas har zuwa wani lokaci

2022-09-03 17:24:28 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne kamfanin sarrafa iskar gas mafi girma a Rasha wato Gazprom, ya sanar da dakatar da tura iskar gas ta bututan sa na “Nord Stream 1” har sai baba ta gani, sakamakon yoyon gas din da ya ce ya gano wani sashe na bututan na yi.

Sanarwar kamfanin dai na zuwa ne ‘yan sa’o’i kadan, bayan da gungun kasashe 7(G7) suka amince su kayyade farashin man kasar Rasha, a wani mataki na rage kudaden shigar da Rashan ke samu wajen gudanar da yaki.

Cikin wani sakon Telegram da kamfanin na Gazprom ya wallafa, ya ce an gano yoyon ne yayin wani aikin hadin gwiwa na gyare gyare da yake aiwatarwa tare da kamfanin Siemens na Jamus, a sashen bututun gas na Portovaya.

Kamfanin Gazprom, ya ce hukumar dake lura da harkokin fasaha da kula da muhallin halittu ta Rasha, ko Rostekhnadzor, ta gabatar masa da gargadi game da matsalar bututun, domin kaucewa aukuwar hadari a injin juya iskar gas din.  (Saminu Alhassan)