logo

HAUSA

Iran na shirya amsarta ga Amurka cikin tsanaki

2022-09-02 13:07:39 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya ce, kasarsa za ta gaggauta shirya amsa cikin tsanaki, wadda za ta ba Amurka game da martaninta kan daftarin yarjejeniyar nukiliyar kasar da Tarayyar Turai ta gabatar.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa, Abdullah bin Zayed Al Nahyan, inda bangarorin biyu suka tattauna game da batutuwan dake jan hankalinsu.

Ya ce Iran ta riga ta nuna kyakkyawan kuduri kuma da gaske take, game da cimma yarjejeniyar mai kwari da dorewa.

Ya kara da cewa, manufar hulda da kasashen waje ta Shugaba Ebrahim Raisin a Iran, na bayar da muhimmanci ga dangantakar kasar da makwabtanta.

A nasa bangare, ministan Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce, a shirye kasarsa take ta inganta dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Iran. (Fa’iza Mustapha)