logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya yi kira da a kara kaimi wajen inganta kwarewa a Afirka

2022-09-01 10:18:08 CMG Hausa

Kwamitin sulhu na MDD ya yi kira da a kara daidaita tsarin hadin gwiwa a tsakanin dukkan abokan hulda masu ruwa da tsaki, musamman ta hanyar inganta kwarewa wajen tinkarar matsalar tashe-tashen hankula, da wanzar da zaman lafiya da sauran kalubale a nahiyar Afirka.

A cikin sanarwar da shugaban kwamitin sulhun majalisar na karba-karba na watan Agusta, kana zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya gabatar, kwamitin mai wakilai 15 ya amince da bukatar kara karfin kwarewar kasashen Afirka yadda ya kamata, da hada kai, da daidaita al'amura, da matakan da suka dace da yanayin kowace kasa da yanki.

Kwamitin ya kuma jaddada muhimmancin mutunta ikon mulkin kai da jagorancin kasashen Afirka, da kuma tallafa musu wajen inganta tsarin doka, da karfafa hukumomin kasa, da gina tsarin shugabanci na-gari, da yayata da kare hakkin dan Adam, da sauransu.

Ya kuma jaddada bukatar raba dabaru, da samar da tallafin kudade kan yayata matakan kwance damara, da sake dunkulewa, ciki har da wadanda suka shafi saki da sake hadewar yaran da ke da alaka da shiga aikin soja ko kungiyoyi masu dauke da makamai, da kuma sake fasalin bangaren tsaro, bayan yanayi na rikici, don tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da tsaro na bai daya. (Ibrahim Yaya)