logo

HAUSA

An bude babban taron cinikayyar yanar gizo na kasar Sin

2022-09-01 16:06:26 CMG Hausa

Yau ne, aka bude babban taron cinikayyar yanar gizo na kasar Sin a babban dakin taron kasa da kasa na kasar Sin dake birnin Beijing, taron da ya kasance daya daga cikin dandamalin tattaunawa na koli na harkokin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 wato CIFTIS na wannan karo, ya samu halartar mataimakin ministan harkokin kasuwancin kasar Sin Sheng Qiuping, inda ya kuma bayyana cewa, cikin watanni 7 na farkon bana, jimllar hajojin da aka sayar ta yanar gizo a kasar Sin, ya kai sama da Yuan triliyan 7, ciki har da kayayyakin yau da kullum da darajarsu ta kai Yuan triliyan 6.3, adadin da ya kai kaso 25.6 cikin dukkanin hajojin da aka sayar a kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, a halin yanzu, cinikayya ta yanar gizo, tana ba da babbar gudummawar farfado da harkokin sayayya a kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)