logo

HAUSA

Gwamnatin Sin ta samar da Yuan biliyan 10 ga manoma domin tabbatar da shuka da girbin hatsi a lokacin kaka

2022-08-30 10:30:00 CMG Hausa

Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin samar da Yuan biliyan 10, domin sake ba da tallafi ga manoma a fannin sayen kayayyakin gona, ta yadda za a taimaka musu wajen gudanar da ayyukan shuka da girbin hatsi a lokacin kaka kamar yadda ake fata. Kuma, ya zuwa yanzu, sau uku ke nan, gwamnatin kasar Sin take samar da tallafin kudi ga manoma a bana, wadanda suka kai Yuan biliyan 40.

A wannan karo, ana ba da tallafin kudi ga manoma na ainihi, musamman ma a fannin gudanar da ayyukan gona a lokacin kaka, da rage kudaden da za su kashe kan kayayyakin gona sakamakon hauhawar farashin kayayyakin gona.

Darektan sashen noma da yankunan karkara na ma’aikatar harkokin kudi ta kasar Sin Wu Qixiu ya bayyana cewa, matakin ba da tallafin kudi ga manoma, zai taimaka wajen rage kudaden da za a kashe a fannin gudanar da ayyukan gona, da kara adadin hatsin da za a samar, da kuma kare moriyar manoma masu gudanar da ayyukan gona, da karfafa musu gwiwar gudanar da harkokin da abin ya shafa, da tabbatar da samun kudin shiga ga manoman hatsi yadda ya kamata, lamarin da ya inganta tushen samun isassun hatsi a duk fadin kasar Sin. (Maryam)