logo

HAUSA

Babban jami’in Sin ya jaddada bukatar raya sabbin kafofin yada labaru

2022-08-30 11:35:35 CMG Hausa

A yau Talata, an kaddamar da taron sabbin kafofin yada labaru na kasar Sin na shekarar 2022 a birnin Changsha dake tsakiyar kasar, inda Huang Kunming, babban jami’i mai kula da harkokin yada labaru na kasar, ya halarci bikin bude taron ta kafar bidiyo, gami da gabatar da jawabi.

A cewarsa, ya kamata a kara yin nazari kan dabaru masu alaka da aikin yada labaru, da sabbin fasahohi na zamanin da muke ciki. Sa’an nan a hanzarta raya bangaren sabbin nau’ikan kafofin yada labaru, don taimakawa kokarin raya kasa. (Bello Wang)