logo

HAUSA

Tsokacin Amurka game da Sin kan batun jihar Xinjiang, tamkar barawo ne dake ihun a kama barawo

2022-08-29 20:21:06 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Litinin cewa, hukumomin da abun ya shafa, na ma'aikatar harkokin wajen Amurka, sun yi wa kasar Sin kazafi, kan yadda take amfani da bayanan karya da ke da alaka da jihar Xinjiang, a wani yanayi mai kamata da barawo dake ihun a kama barawo.

Zhao Lijian, ya ce a halin yanzu, an tabbatar da tsaro da zaman karko a Xinjiang, kuma jihar tana samun ci gaba yadda ya kamata. Kaza lika jama'ar jihar suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali, wanda hakan shi ne martani mafi kyawu, kuma mafi karfi ga farfagandar bayanan karya na Amurka don gane da jihar.

Baya ga haka, kakakin ya jaddada cewa, duk da yawan karairayi da Amurka ke kirkira game da jihar Xinjiang, ba za ta makantar da idanun duniya ba, kana ba za ta ruguza zaman jituwa, da zaman karkon jihar ba, kuma ba za ta iya boye muryar adalci ta kasashen duniya, da ke goyon bayan kasar Sin ba. Maimakon haka, Amurka za ta kara rasa amincewar da take da ita a tsakanin sassan kasa da kasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)