logo

HAUSA

Falastinu ta yi tir da kutsen da Yahudawa suka yi wa masallacin Al-Aqsa

2022-08-29 10:26:02 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu, ta yi tir da kutsen da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna suka yi wa masallacin Al-Aqsa dake tsohon birnin Kudus, ta wata kofa da kafafen yada labarai na kasar suka ce, musulmai ne kadai ke bi.

A cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA, wannan shi ne karo na farko da ‘yan sandan Isra’ila suka kyale Yahudawan suka shiga harabar wajen ibadar, ta daya daga kofofin dake isa masallacin Al-Aqsa.

Ma’aikatar ta ce wannan mataki da ba a yi tsammani ba, ya take ka’idar matsayin masallacin, inda ta ce Falasdinu za ta dora alhakin duk wani abu da zai biyo baya kan gwamnatin Isra’ila da sakamakon fin karfin da take nunawa kan birnin na Kudus da wuraren ibada na musulmai, musammam masallacin Al-Aqsa.

Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito daraktan masallacin Al-Aqsa, Sheikh Omar Kiswani na cewa, kutsen da aka yi wa masallacin Al-Aqsa ya take yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Isra’ila da Jordan, game da harkokin masallacin. (Fa’iza)