logo

HAUSA

Ana ci gaba da kokarin kyautata rayuwar al’ummun Xinjiang

2022-08-27 16:17:24 CMG Hausa

Rahotannin da aka gabatar yayin taron watsa labaran da aka shirya da safiyar yau Asabar, mai taken “Sakamakon da aka samu a yankin Xinjiang na kasar Sin a cikin shekaru goma da suka gabata” sun nuna cewa, gwamnatin yankin Xinjiang tana ci gaba da kokari domin kara kyautata rayuwar al’ummunta da yawansu ya kai miliyan 25.85 a fannonin samun aikin yi, da kiwon lafiya, da kyautata sharadin mallakar gidaje da sauransu.

An labarta cewa, matsakacin yawan sabbin guraben ayyukan yi da aka samar a kowacce shekara tsakanin shekarar 2012 zuwa 2021 a yankin ya kai sama da dubu 460, kuma matsakacin yawan manoman yankin da suka tafi sauran yankunan dake fadin kasar domin aiki, ya kai fiye da miliyan 2.85, kuma kusan kowanne ma’aikacin yankin yana iya samun aikin yi. Baya ga haka, matsakacin karuwar adadin kudin shiga a birane da garuruwan yankin Xinjiang, ya kai kaso 7.9 bisa dari, a kauyuka kuwa ya kai kaso 9.5 bisa dari a cikin shekaru goma da suka gabata.

Bugu da kari, an gina isassun makarantun renon yara a fadin yankin, inda yara kanana suke samun kulawa kyauta kafin su shiga makarantar firamare, haka kuma an cimma burin samar wa yaran kauyuka iznin shiga makarantar dake kusa da gidajensu.

Hakazalika, gaba daya gwamnatin yankin Xinjiang ta samar da sabbin gidaje ga al’ummun yankin na kabilu daban daban da yawansu ya kai sama da miliyan 10 tun daga shekarar 2012. (Jamila)