logo

HAUSA

Kwararru: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Na Bunkasa Ci Gaban Nahiyar Afirka

2022-08-25 11:05:11 CMG Hausa

Wasu masu bincike, kuma kwararru game da al’amuran kasa da kasa na yankin gabashin Afirka, sun bayyana shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, a matsayin manufar dake ingiza ci gaban nahiyar Afirka. Kwararrun sun yi tsokacin ne a jiya Laraba, yayin taron yini guda da ya gudana ta kafar bidiyo, mai taken "Muhimmancin shawarar ziri daya da hanya daya ga nahiyar Afirka."

Daya daga cikin kwararrun Frederick Golooba Mutebi daga kasar Uganda, ya ce shawarar ziri daya da hanya daya, ta zamo ginshikin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da rage matsalar karancin guraben ayyukan yi, da bunkasa cinikayya da dai sauran su.

Mr. Mutebi ya ce "Sin ba ta da nufin wawashe arzikin Afirka, sabanin yadda kasashen yamma ke zargi. Kuma idan aka dubi ci gaban da nahiyar Afirka ke samu a fannin samar da ababen more rayuwa, za a fahimci irin taimako da shawarar ziri daya da hanya daya ke baiwa nahiyar. Sin na samar da agaji irin wanda kasashen Afirka ke bukata”.

A nasa bangare kuwa, masani a fannin alakar kasa da kasa daga kasar Kenya Adhere Cavince, cewa ya yi shawarar ziri daya da hanya daya, ta baiwa kasar Sin damar raba dabarun ci gaban ta da sauran kasashen Afirka masu tasowa. Ya ce gwamnatin Kenya na aiki kut da kut da kasar Sin, wanda hakan ya haifar da nasarar kammala layin dogo da ya hade biranen Mombasa da Nairobi, aikin da ke taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar Kenya.

Cavince ya kara da cewa, cikin shekaru goma da suka gabata, Sin da kasashen Afirka sun zamewa juna abokan huldar cinikayya yayin da kuma shawarar ziri daya da hanya daya ta budewa sassan 2 sabbin kofofin bunkasa hadin gwiwa.   (Saminu Alhassan)