logo

HAUSA

An harbe mutane 2 a harin bindiga na Washington DC

2022-08-25 11:02:37 CMG Hausa

 

Rundunar ’yan sandan Washington DC gundumar kwalambiya na Amurka ta ce, wasu mutane 2 sun rasu, kana karin wasu mutane 3 sun jikkata, sakamakon harbe-harben bindiga da ya wakana, da misalin karfe 1 saura mintuna 10 na daren Laraba, a yankin North Capitol, da O Street, dake arewa maso yammacin birnin.

’Yan sanda sun ce sun samu kiran gaggawa zuwa wurin da aka ji amon harbe-harben, kuma da isarsu suka tarar da gawawwakin mutane 2, yayin da sauran mutum 3 ke samun kulawa a asibiti, ko da yake ba su bayyana yanayin jikkatar masu raunuka ba. (Saminu Alhassan)