logo

HAUSA

Jami’in Kasar Sin Ya Yi Gargadi Game Da Hadarin Sake Tsunduma Sabon Yakin Cacar Baka

2022-08-25 11:08:16 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi gargadi game da hadarin sake tsundumar duniya cikin yanayi na yakin cacar baka. Jami’in wanda ya yi kashedin a jiya Laraba, ya kuma jaddada muhimmancin kare tsarin daidaito na duniya.

Zhang, wanda ke tsokacin yayin zaman kwamitin tsaron MDD da ya gudana game da rikicin Ukraine, ya ce yanayin matsi da ci gaban duniya ke fuskanta, na nuni ga bukatar lura, da aiki tukuru, wajen ganin an kawar da rarrabuwar kawuna, da kaucewa rikici da fito na fito.

Wakilin na kasar Sin ya ce, cikin sama da shekaru 30 da suka gabata, tun bayan kawo karshen yakin cacar baka, kungiyar tsaro ta NATO ke ci gaba da fafada tasirinta zuwa gabashi, duk da cewa hakan bai wani kara samarwa Turai karin tsaro ba, sai ma rura wutar rikici da hakan ke haifarwa.

Ya ce bai dace kasashe masu tasowa su rika dandana tasirin riciki, da rigingimun dake wakana tsakanin manyan kasashen duniya ba. Kuma kasashen na da damar zabar manufofinsu na waje, kana bai dace a tilasta musu zabar wani bangare ba.

Zhang ya kara da cewa, bai dace batun amincewa da ka’idojin MDD, da martaba ikon mulkin kai, da tsaron yankunan kasashe ya zama a fatar baki kadai ba. Maimakon haka, kamata ya yi dukkanin kasashe su amince, tare da rungumar wadannan ka’idoji na cudanyar kasa da kasa bisa yakini.

Daga nan sai ya bayyana irin yadda al’ummar Sinawa ke da matukar fahimta, da imani game da ’yancin kai da ikon tsaron yankunan kasar su, saboda irin wayewar da suka samu daga tarihi. Ya ce har kullum kasar Sin na nacewa manufar martaba ikon mulkin kai, da tsaron yankunan sauran kasashen duniya, kuma a shirye take ta kare kimar mulkin kai, da dunkulewar daukacin yankunanta. (Saminu Alhassan)