logo

HAUSA

Sin ta bukaci a kara kaimi don samun girbi mai armashi yayin da ake fama da tsananin zafi a wasu sassan kasar

2022-08-23 19:53:42 CMG Hausa

Hukumomi a kasar Sin sun bukaci a dauki matakan da suka dace wajen tunkarar tasirin fari, domin samun girbi mai armashi a lokacin kakar bana.

Wata sanarwa da ma’aikatar kula da aikin gona da yankunan karkara da ta albarkatun ruwa da mai kula ayyukan gaggawa da hukumar kula da yanayi na kasar Sin suka fitar, ta ce tun daga karshen watan Yuli ake fama da tsanantar zafi a yankunan kudancin kasar Sin, lamarin dake barazana mai tsanani ga girbi a bana. (Fa’iza Mustapha)