logo

HAUSA

Sin ta nuna matukar rashin jin dadi game da ziyarar gwamnan jihar Indiana a yankin Taiwan

2022-08-23 11:10:50 CMG HAUSA

 

Gwamnan jihar Indiana ta Amurka Eric Holcomb, yana ziyara a yankin Taiwan na kasar Sin. Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ba ta amince da duk wani matakin da Amurka ta dauka, na yin mu’ammala a siyasance, tsakaninta da yankin Taiwan ba. Kuma Sin tana matukar rashin jin dadin hakan.

Wannan jami’i ya jaddada cewa, yankin Taiwan wani bangare na kasar Sin da ba za a iya ware shi ba. Kuma batun yankin batu ne mafi muhimmanci a huldar Sin da Amurka. Don haka Sin ta kalubalanci Amurka, da ta nace ga ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, da tsayawa tsayin daka kan sanarwoyi uku na tsakaninsu, kuma ta daina mu’ammala a siyasance da mahukuntan yankin Taiwan. (Amina Xu)