logo

HAUSA

An kammala shirye shiryen bikin cinikayyar hidimomi na 2022

2022-08-23 20:13:15 CMG Hausa

Bikin cinikayyar hidimomi na 2022, zai gudana a cibiyar taro ta kasar Sin da kuma yankin Shougang daga ranar 31 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba. Rahotanni na cewa, an kara inganta matakin kwarewar hidimomi da shigar kasashen duniya, bikin na bana. Muhimman baki daga ciki da wajen kasar Sin 189 ne suka ba da tabbacin za su halarci bikin, kuma kasashe da hukumomin kasa da kasa 71 sun kafa wurare baje hidimomi da sunan kasa ko hedkwata. Daga cikin kasashe masu halarta, wasu 10 da suka hada da Burundi da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun kafa wuraren nune-nune da sunan kasarsu a karon farko. (Fa’iza Mustapha)