logo

HAUSA

Sin ta zama daya daga cikin kasashen dake sahun gaba a kirkire-kirkire

2022-08-19 16:32:44 CMG Hausa

A cikin shekaru 10, adadin yankunan misali na gudanar da sana’ar kirkire-kirkire a kasar Sin, ya karu daga guda 3 zuwa guda 23, kana, yawan kamfanonin dake raya sabbin fasahohin zamani ya karu, daga dubu 49 a shekaru sama da 10 da suka wuce, zuwa dubu 330 a shekara ta 2021.

A shekaru 10 da suka gabata kuma, muhimman wuraren dake yin kirkire-kirkire a kasar Sin ya fadada, daga yankunan bakin teku dake gabashin kasar, zuwa yankunan tsakiya da yammacin kasar, kuma a duk sassan kasar, ana iya samunsu.

Tun daga shekara ta 2013, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan Adam da dama, wadanda ake iya amfani da su don daukar hotuna iri-iri, don gano mabambantan yankunan kasar.

A wasu shekaru da suka wuce kuma, yankin Qianhai dake birnin Shenzhen a kudancin kasar Sin, ya zama daya daga cikin yankunan da suka samu sauye-sauye mafi girma a kasar Sin. Kuma a cibiyar tattalin arziki dake yankin Qianhai, adadin sassan tattalin arzikin da suka shiga ya kai 195 a cikin kasa da shekara daya.

Ingantaccen tsarin yin kirkire-kirkire, yana taimakawa sosai ga saurin ci gaban tattalin arzikin yankin Qianhai. A shekara ta 2021, yawan GDPn yankin ya riga ya kai kudin Sin Yuan biliyan 175.57.

Harkokin yin kirkire-kirkire, ba kawai sun canza halin da ake ciki a kowane sashi na kasar Sin ba ne, har ma suna jagorantar dukkanin sassan kasar zuwa gaba. A yanzu haka, jiragen kasa masu saurin gudu, da tsarin sadarwar zamani ta 5G a kasar Sin suna kan gaba a duniya, har ma an cimma tudun-dafawa a fannin harba kumbunan dakon dan Adam zuwa sararin samaniya, da binciken duniyar Mars, kana sana’ar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi ta kasar Sin tana kan gaba a duk duniya. (Murtala Zhang)