logo

HAUSA

Shugaban Kenya ya sha alwashin mika mulki cikin lumana

2022-08-19 13:28:56 CMG Hausa

Shugaban kasar Kenya mai shirin barin gado Uhuru Kenyatta ya sha alwashin mika mulki ga zababbiyar gwamnati cikin lumana, biyowa bayan zazzafan zaben kasar da ya gudana a farkon watan nan.

Tuni dai shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta ko IEBC Mr. Wafula Chebukati, ya ayyana mataimakin shugaban kasar mai ci William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben. Inda ya yi nasara kan babban abokin hamayyarsa Raila Odinga, da kaso 50.49 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada.

A ranar Talatar da ta gabata, Mr. Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben da aka bayyana, yana mai shan alwashin garzayawa kotu, da fatan kotu za ta soke sakamakon zaben.

Dukkanin mai kalubalantar sakamakon zaben dai na da wa’adi har zuwa ranar Litinin din makon gobe, da ya shigar da korafinsa gaban kotun kolin kasar, wadda kuma za ta zartas da hukuncin ta cikin makwanni 2.

Idan har kotun kolin ta soke zaben, za ta ba da umarnin sake kada kuri’u cikin kwanaki 60.  (Saminu Alhassan)