logo

HAUSA

An cimma daidaito a taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministocin FOCAC na 8

2022-08-19 20:05:52 CMG Hausa

A yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi bayani game da sakamakon da aka cimma a taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministocin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka FOCAC na 8, inda ya bayyana cewa, yanayin taron ya yi kyau kuma yana da ma’ana sosai. Bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi da cimma daidaito kan yadda za a aiwatar da sakamakon taron ministocin FOCAC na 8 da kuma inganta hadin gwiwar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, an zartas da hadaddiyar sanarwa a gun taron, wanda ya kunshi ra’ayi daya da Sin da Afirka suka cimma kan martaba ka’idojin kundin tsarin MDD, da nuna adawa da tsoma baki daga waje da saka takunkumi daga bangare daya da kuma nuna wariyar launin fata, da kuma kiyaye yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19 da dai sauransu, wannan ya shaida cewa, bangarorin biyu wato Sin da Afirka, suna nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafarsu, ya kuma nuna aniyar Sin da Afirka ta hada hannu don gina al'ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani. Bangaren Afirka ya sake nanata bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan babbar manufar kasar Sin ta dinkuwar kasa, da goyon bayan kokarin kasar Sin na kiyaye 'yancin kan kasa da cikakkun yankunanta, matakin da kasar Sin ta yaba sosai. (Zainab)