logo

HAUSA

Ana baje kolin mutum-mutumin inji na kasa da kasa a Beijing

2022-08-19 11:06:00 CMG Hausa

An kaddamar da bikin baje-kolin ire-iren mutum-mutumin inji na kasa da kasa na shekara ta 2022 a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, wanda ya samu halartar kamfanonin samar da mutum-mutumin inji, gami da cibiyoyin nazari sama da 130.

Ana baje-kolin wasu mutum-mutumin inji sama da 500 a bikin bana, kana za’a bullo da wasu sabbin nau’o’in mutum-mutumin inji fiye da 30 a wajen bikin, al’amarin da zai shaida nasarorin kirkire-kirkire, da fasahohin zamani a fannin mutum-mutumin inji.

“Cibiyoyin da suke nuna goyon-baya ga taron mutum-mutumin inji a bana sun dara na shekarun baya.”

In ji maitaimakin babban mai bada umurni ga babban taron, wanda kuma shi ne mataimakin sakatare-janar na kungiyar nazarin kayan laturonin kasar Sin, Liang Liang. Ya ce, babban taron mutum-mutumin inji na kasa da kasa, na kara taka rawa a duk fadin duniya, duba da yadda mutum-mutumin inji ke kara samun karbuwa a wasu sana’o’i da dama.

An kuma gudanar da babbar gasar fidda gwani a fannin mutum-mutumin inji ta duniya ta bana, wadda ta kunshi wasu fannoni hudu, ciki har da gasar amfani da mutum-mutumin inji, da gasar tsara fasalin mutum-mutumin inji ta matasa da sauransu. (Murtala Zhang)