logo

HAUSA

Sin: Hadin Gwiwar Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Haifar Da Sakamako Mai Kyau Da Fa'ida

2022-08-18 21:00:54 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya shaiadawa taron manema labarai a yau Alhamis cewa, a cikin shekaru 8 da suka gabata, tun bayan da aka gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya zuwa yanzu, kasar Sin ta yi aiki tare da kasashen da abin ya shafa, wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna bisa ka'idar yin shawarwari mai zurfi, da ba da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna, kana ta cimma nasarori masu tarin yawa.

Wang Wenbin ya kara da cewa, ya zuwa ranar 4 ga watan Yulin bana, kasar Sin ta rattaba hannu kan muhimman takardun hadin gwiwa da kasashe 149 da kungiyoyin kasa da kasa 32, don gina shawarar cikin hadin gwiwa, inda aka gudanar da ayyukan hadin gwiwa fiye da 3,000 da zuba jarin da ya kai kimanin dalar Amurka triliyan 1.

A watanni shida na farkon wannan shekara, darajar cinikayyar kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen dake aiwatar da shawarar, ta kai kudin Sin yuan triliyan 6.3, wanda ya karu da kashi 17.8 bisa 100 kan na shekarar 2021. Kana kuma jimillar jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye wanda bai shafi kudi ba a kasashen dake cikin shawarar, ta kai kudin Sin yuan biliyan 65.03, karuwar kashi 4.9 bisa 100.(Ibrahim)