logo

HAUSA

Li Keqiang ya jaddada muhimmancin sanya sabon kuzari don samar da ci gaba

2022-08-18 10:25:59 CMG Hausa

Daga ranar 16 zuwa 17 ga watan nan, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ziyarci birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, ya dace a bi ra’ayin jagorancin shugaba Xi Jinping, irin na gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, da tabbatar da sabon ra’ayin samar da ci gaba, da daidaita ayyukan kandagarkin annobar COVID-19, da raya tattalin arzikin kasa, da ci gaba da aza tubali mai inganci na farfado da tattalin arzikin kasar, a wani kokari na tabbatar da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma, da kyautata rayuwarsu ta yau da kullum, don raya tattalin arziki yadda ya kamata.

Li ya ce, bude kofa ga kasashen waje, babbar manufa ce ta kasar Sin, kana, komai sauyawar halin da ake ciki a kasa da kasa, ya dace kasar Sin ta tsaya ga fadada bude kofarta ga kasashen waje, da ci gaba da amfani da kasuwannin cikin gida da na waje, don neman samun moriya tare.

Firaminista Li, ya kuma sake nanata cewa, kasar Sin tana samar da goyon-baya a fannin manufofi irin daya, ga kamfanoni daban-daban, ciki har da na kasa, da masu zaman kansu, da masu jarin waje da sauransu. (Murtala Zhang)