logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a birnin Shenyang

2022-08-18 10:54:31 CMG Hausa

Da yammacin jiya Laraba ne babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi rangadin aiki a birnin Shenyang, fadar mulkin lardin Liaoning dake yankin arewa maso gabashin kasar Sin, inda ya ziyarci kamfanin kera na’urar mutum mutumi na Xinsong, da unguwar Mudan ta titin Santaizi, domin ganewa idanun sa yadda ake ingiza kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kara karfafa gina kungiyoyin JKS, da kyautata aikin samar da hidima a unguwar da sauransu. (Jamila)