logo

HAUSA

Ra’ayin shugaba Putin kan batun Taiwan ya shaida hadin gwiwa mai inganci dake tsakanin Sin da Rasha

2022-08-17 20:01:35 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin tana matukar yabawa da kalaman baya-bayan da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi, game da ziyarar da Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan, ra’ayin shugaba Putin ya shaida hadin gwiwa mai inganci bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Rasha, da yadda kasashen biyu suke nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu.

Rahotanni na cewa, shugaba Putin ya bayyana a jiya cewa, ziyarar Pelosi a yankin Taiwan, yunkuri ne da aka tsara na dogon lokaci, kuma yana daya daya cikin manufofin kasar Amurka na kawo illa ga zaman lafiya da tada zaune tsaye a yankin, wannan ya shaida cewa, kasar Amurka ba ta girmama ikon mulkin sauran kasashe, da watsi da nauyin dake a wuyanta.

Game da wannan batu, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, tun bayan da Pelosi ta kai ziyara a yankin Taiwan, kasashe fiye da 170 sun bayyana ra’ayoyinsu, inda suka tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da nuna goyon baya ga Sin wajen kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankunanta. Sin tana son ci gaba da aiki tare da kasashen duniya wajen kare manufofi da ka’idojin MDD, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya. (Zainab)