logo

HAUSA

Jakadan Morocco: Morocco Tana Martaba “Manufar Sin Daya Tak A Duniya”

2022-08-14 15:56:09 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, jakadan kasar Morocco dake nan kasar Sin Aziz Mekouar, ya nanata yadda masarautar kasarsa take martaba “manufar Sin daya tak a duniya”, a matsayin tushen dangantakar dake tsakanin kasashen abokan juna.

Mekouar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Moroccon dake nan kasar Sin ya fitar game da batun yankin Taiwan na kasar Sin.

A cikin sanarwar, Mekouar ya bayyana cewa, a tsakanin bangarorin biyu da kuma na kungiyoyin kasa da kasa, Morocco za ta ci gaba da goyon bayan kasar Sin kan wannan batu, tare da jaddada matsayinta. Yana mai cewa, matsayin masarautar ya shafi mutunta ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunanta, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe.

Ya kara da cewa, Morocco ta yaba da goyon baya da matsayin kasashe abokai na goyon bayan kare yankinta.

Dangane da dangantakar da ke tsakanin kasar Morocco da kasar Sin kuwa, jakadan ya bayyana cewa, kasarsa tana mai da hankali sosai, kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai jaddada cewa, kasashen biyu sun kuduri aniyar karfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.

Jakada Mekouar ya nuna cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)”

ta bude sabbin damammaki na kasuwanci da zuba jari, da karin damammaki da suka dace da sabon tsarin masarautar game da raya kasa.(Ibrahim)