logo

HAUSA

Sin ta sanyawa mataimakiyar ministan sufurin kasar Lithuania takunkumi

2022-08-13 17:10:15 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya sanar da kakabawa mataimakiyar ministan sufuri da sadarwa na kasar Lithuania Agne Vaiciukeviciute takunkumi. Hakan dai ya biyo bayan ziyarar da jami’ar ta kai yankin Taiwan, lamarin da ya keta alfarmar manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, da keta hurumin mulkin kai, da tsaron yankunan kasar Sin.

Takunkumin da kasar Sin ta kakabawa Vaiciukeviciute, ya hada da dakatar da dukkanin wata musaya, tsakanin bangaren Sin da ma’aikatar da jami’in ke wakilta, da kuma jingine duk wata hadin gwiwa da musaya da Lithuania, a fannonin sufurin hanyoyin mota na kasa da kasa.  (Saminu Alhassan)