logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bayyana ra’ayin bangaren Sin game da kyautata tsarin kasashen dake da alhakin rubuta daftarin kudurin MDD

2022-08-12 16:36:46 CMG HAUSA

 

Mataimakin wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya yi jawabi a yayin taron salon Aria da kwamitin sulhu na MDD ya shirya game da kasashe wadanda suke da alhakin rubuta daftarin kudurin MDD, inda ya bayyana ra’ayin bangaren Sin game da inganta wannan salo na Aria.

Geng Shuang ya ce, kamata ya yi kasashe wadanda suke da alhakin rubuta daftarin kudurin MDD su saurari shawarwari ko ra’ayoyin kasashe masu ruwa da tsaki, su kuma kula da bukatunsu a maimakon raina su ko yin watsi da ra’ayoyinsu.

Mr. Geng ya ce, a ’yan shekarun baya, kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da Somaliya da Kongo Kinshasa da Afirka ta Tsakiya da sauransu, sun gabatar da shawarwari daya bayan daya, game da soke takunkumin hana mallakar makamai da dai sauransu da aka kakkaba musu. Kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU da sauran kasashen Afirka da galibin kasashe mambobin kwamitin sulhun MDD ma sun amince da kuma goyon bayan shawarwarin. Ya ce kamata ya yi kasashen dake da alhakin rubuta daftarin kudurin MDD su sanya kwamitin sulhu ya dauki matakai masu dacewa da wuri, wajen duba tsarin kakkaba takunkumi daga dukkan fannoni, ta yadda za a iya yin watsi da takunkumai wadanda ba su dace da yanayin da ake ciki ba.

Geng Shuang ya nuna cewa, wasu kasashe kalilan sun dade suna mamaye wannan alhaki na rubuta daftarin kudurin MDD. Sabo da haka, bangaren Sin ya ba da shawarar kyautata tsarin zabar kasashen dake da alhakin rubuta daftarin. (Safiyah Ma)