logo

HAUSA

Rundunar PLA reshen gabashi ta kammala atisayenta a kewayen tsibirin Taiwan cikin nasara

2022-08-11 21:17:47 CMG Hausa

Kakakin rundunar‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA a takaice reshen gabashi Shi Yi, ya bayyana a jiya Laraba cewa, dakarun rundunar sun kammala atisayen soji da aka tsara gudanarwa, a kewayen sassan ruwa da samaniyar tsibirin Taiwan na kasar Sin.

Shi Yi ya ce atisayen, ya kunshi ayyuka daban daban na gwajin karfin rundunar, a fannin kaddamar da hare hare cikin hadin gwiwa. Kuma rundunar za ta ci gaba da lura da irin yanayin zirin na Taiwan. Kana za ta ci gaba da gudanar da horon soji na zama cikin shirin yaki, da tsara ayyukan sintiri a zirin na Taiwan, da nufin tabbatar da kare ikon mulkin kai, da tsaron daukacin sassan kasar Sin.   (Saminu Alhassan)