logo

HAUSA

Tawagar MINUSCA a CAR ta tura dakarun gaggawa domin kare fararen hula

2022-08-11 10:48:51 CMG HAUSA

 

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (MINUSCA), ta tura dakarun kai dauki gaggawa, domin kare fararen hula a lardin Bamingui-Bangoran.

Stephane Dujarric, babban mai magana da yawun magatakardan MDD Antonio Guterres, wanda ya sanar da haka, ya bayyana cewa, tawagar dake aiki a Jamhuriyar tsakiyar Afirka, ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa garin Ndele, a daidai lokacin da ake samun rahotannin yiwuwar kai hare-hare daga kungiyoyin masu dauke da makamai.

Dujarric ya ce, an ci gaba da sauraren kara kotun hukunta manyan laifuka ta musamman, bisa goyon bayan tawagar a ranar Litinin, a shari'ar da ake zargin mambobin kungiyar 3R guda uku da aikatawa. Karar ta shafi kashe fararen hula kusan 40 a Lemouna da Koundjili a watan Mayun shekarar 2019.

Kakakin ya ce MINUSCA na ci gaba da karfafa hanyoyin kare al'umma, ciki har da na Ouadda-Djalle da ke lardin Vakaga, ta hanyar ba da horo kan tsarin gargadin wuri, wanda ya taimaka wajen inganta tsaro a yankin. Wannan na daga cikin ci gaba da goyon bayan da hukumomin kasa ke bayarwa a fannin karfafa tsaro, da adalci da rikon amana a cikin kasar. (Ibrahim)