logo

HAUSA

Kasar Sin ta kasance ta biyu a duniya a yawan na'urorin makamashin nukiliya dake aiki da wadanda ake ginawa

2022-08-10 11:13:54 CMG Hausa

     

Mataimakin darektan hukumar tsaron makamashin nukiliya ta kasa, kana daraktan sashen sa ido kan makamashin nukiliya na kasar Sin, Tang Bo ya bayyana cewa, ya zuwa watan Yunin shekarar 2022, kasar Sin tana da rukunin tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya 54 dake aiki, baya ga tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya guda 23 da ake ginawa, abin da sanya ta zama ta biyu a duniya.

Tang Bo ya gabatar da wannan bayani ne, a yayin bikin bude taron kasa da kasa kan fasahar nukiliya karo na 29 da aka gudanar a jiya.

Ya bayyana cewa, ci gaban makamashin nukiliya, ya ba da gudummawa mai yakini, da fa'ida a fannin tabbatar da samar da makamashi, da inganta muhalli, da manufar kololuwar fitar da iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu, da daidaita hayakin carbon.

A kokarin da take yi na bunkasa makamashin da ake iya sabuntawa, kasar Sin ta bullo da wani tsari mai inganci, da tsaro da kuma tsari mai kyau kan makamashin nukiliya. A halin yanzu, ana samun ingantuwar alkaluma a tashohin nukliyar dake aiki wato ( NPPs) wadanda ake ce suna daga cikin mafiya ci gaba a duniya

An gudanar da taron fasahar nukiliya na kasa da kasa karo na 29 a biranen Beijing da Shenzhen daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Agusta, bisa taken "Kwarewar makamashin nukiliya na taimakawa daidaita iskar Carbon a nan gaba". Sama da kwararru da masana 1,200 daga kasashe sama da 20 ne suke halartar taron. (Ibrahim Yaya)