logo

HAUSA

Batun Taiwan zai kammala ne da dinkuwar kasar Sin baki daya

2022-08-10 08:43:14 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, matakin da galibin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka bayyana shi a matsayin tsokana da neman tayar da zaune tsaye a mashigin ruwan Taiwan.

Taiwan dai wani bangare ne na kasar Sin tun kusan yau shekaru 1,800 da suka gabata. Sannan a shekarar 1943, shugabannin kasashen Sin da Amurka da Burtaniya suka bayar da sanarwar Alkahiran kasar Masar, wadda ta bayyana karara cewa, dukkan yankunan da kasar Japan ta sace daga kasar Sin kamar Taiwan a cikin yakin da aka yi tsakanin Sin da Japan a karshen karnin 19, dole ne ta maido su ga kasar Sin.

Ita ma yarjejeniyar Potsdam ta shekarar 1945 ta tabbatar da cewa, wajibi ne a aiwatar da sharuddan dake kunshe cikin sanarwar Alkahira. Kana a shekarar 1971, babban zauren MDD ya amince da kudiri mai lamba 2758, wanda ya amince da wakilcin gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, a matsayin halastacciyar gwamnati da za ta wakilci kasar Sin a MDD, a waje guda, ta sake jaddada cewa, yankin Taiwan wani bangare ne na jamhuriyar jama’ar Sin, ba a iya balle shi daga kasar Sin ba.

Bugu da kari, a lokacin da Sin da Amurka suka kulla huldar jakadanci a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1979, sassan biyu sun amince cikin wasu sanarwoyin hadin gwiwa cewa, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ce halastacciyar gwamnatin Sin, yankin Taiwan wani bangare ne na jamhuriyar jama’ar Sin, ba a iya balle shi daga kasar Sin ba, kasar Amurka ta mutunta cikakken yankin kasar Sin da ikonta na mulkin kasar.

Duk da wadannan shaidu da bayanai na tarihi, Pelosi ta kau da kai ta gudanar da wannan haramtacciyar ziyara, domin neman cimma wani buri na siyasa da neman tayar da zaune tsaye da keta ka’idar kasar Sin daya tak a duniya, da ma dokoki na kasa da kasa. Lamarin da ya gamu da yin Allah wadai daga bangarori da dama a ciki da wajen kasar Sin.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jaddada matsayin kasar Sin da batun yankin Taiwan kan wannan ziyara, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan kammala taron ministocin wajen kungiyar ASEAN. Har kullum kasar Sin tana nacewa ga kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma yankin Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba.

Yunkurin Amurka na dakile kasar Sin ta hanyar fakewa da batun yankin Taiwan, ba zai taba yin nasara ba, kuma ba zai iya canza yanayin tarihi dake tabbatar da cewa, babu makawa Taiwan zai dawo karkashin ikon kasar Sin, tare da zaburar da al'ummar Sinawa biliyan 1.4, da su hada kai, tare da gaggauta gina babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani mai sigar kasar Sin. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)