logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kasashen dake bin shawarar “Ziri daya da hanya daya” na 2022

2022-08-09 17:08:29 CMG Hausa

A yau ne, aka gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kasashen dake cikin shawarar “Ziri daya da hanya daya” na shekarar 2022 a birnin Xi’an dake jihar Shaanxi ta kasar Sin, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban hukumar yada manufofin kwamitin kolin JKS Huang Kunming, ya halarci taron tare kuma da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Huang Kunming ya bayyana cewa, raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa wani babban shiri ne da Shugaba Xi Jinping ya gabatar, bisa tsarin bunkasuwar duniya da bukatun ci gaban da aka cimma a wannan zamani, da inganta gina al'umma mai makomar daya ga daukacin bil-Adama.

Kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa da ba za a iya maye gurbinsu ba wajen yada bayani, da inganta yarda da juna da kulla yarjejeniya da sauransu.

Raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” ba zai samu ba, sai da hadin kai da himma na kafofin watsa labarai na kasashe daban daban, da kuma sadarwa na zahiri da hadin gwiwa da juna.

A nan gaba, ya yi fatan galibin abokan kafofin watsa labarai, za su gada da kuma yada ruhin hanyar siliki, da himmatuwa wajen yada ra'ayin wayewar kai na daidaito, da koyi da juna, da tattaunawa da hadin kai, da magana da kalamai masu dacewa, don neman ci gaba cikin hadin gwiwa, da kara kaimi don cin nasara, da kuma yadda kafofin watsa labarai za su bayar gudummawa don gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” mai inganci tare. (Safiyah Ma)