logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin: Jakadun kasashen musulmi a Sin sun jinjinawa dabarun Sin na jagorancin Xinjiang

2022-08-08 21:17:05 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya gabatar da bayani game da ziyarar da jakadun wasu kasashen musulmi dake kasar Sin suka kai jihar Xinjiang, inda jakadun suka jinjinawa dabarun kasar Sin na jagorancin al’ummun Xinjiang yadda ya kamata.

Da yake karin haske kan ziyarar da jakadun suka kai Xinjiang, tsakanin ranekun 1 zuwa 5 ga watan nan na Agusta, Wang Wenbin ya ce jami’ai da jakadun kasashen musulmin 30, sun jinjinawa dabarun kasar Sin na jagorancin Xinjiang cikin nasara. Kaza lika sun yaba da irin kwazon da jihar ta yi, na ingiza nasarorin da aka samu a fannin raya tattalin arziki, da dunkulewar sassan kasa da sauran fannoni.

Wang Wenbin ya ce “Gani ya kori Ji", kuma ba wannan ne karon farko da tawagar wakilan kasashen waje ta kai ziyara Xinjiang, tare da jinjinawa nasarar da jihar ta cimma ba. Don haka batun ko ana kare hakkokin bil adama, da ‘yancin bin addinai a Xinjiang, al’ummar jihar ne ya dace su fayyace hakan, kuma al’ummun kasa da kasa ma sun gani.

Cikin kasashen da jami’ai da jakadunsu suka samu ziyartar jihar Xinjiang a wannan karo, akwai na kasashen Algeria, da Guinea Bissau, da Mauritania, da masarautar Saudiyya da Pakistan da sauran su. (Saminu Alhassan)