logo

HAUSA

Kowa ya san ainihin makasudin Pelosi kan hujjarta ta “demokuradiyya”

2022-08-08 21:31:56 CMG Hausa

Kwanan baya, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, bisa hujjar da ta fake da ita, wato “goyon-bayan demokuradiyya”. Amma mazauna yankin Taiwan sun san ainihin makasudinta, inda masu zanga-zanga a Taiwan suka bayyana cewa, Pelosi ta yi wannan ziyara ne domin neman cimma muradun ita kanta, da na jam’iyyar siyasa, gami da ta Amurka.

Pelosi ta ziyarci Taiwan ne ba don kiyaye “demokuradiyya” ba, sai don hura wutar kawowa kasar Sin baraka, da keta demokuradiyya.

Mecece demokuradiyya? Ma’anarta ita ce, al’umma su iya yanke shawara kan manyan batutuwan kasa. A kan batun Taiwan, matsayin al’ummar kasar Sin baki daya a bayyane yake, wato tsayawa kan mulkin kai da cikakkun yankunan kasa, kana, ba za su yarda da duk wani yunkuri na balle Taiwan daga kasar Sin ba. In dai da gaske Pelosi tana son kiyaye demokuradiyya ne, ya dace ta girmama muradun daukacin al’ummar kasar Sin, wanda ya kai kashi 20 bisa 100 na yawan al’ummar duk duniya. Amma Pelosi ba ta yi hakan ba, al’amarin da ya sa ta zama akasin demokuradiyya.

A kwanan nan, martanin da kasar Sin ta mayar ya samu babban goyon-baya daga kasa da kasa. Matakan da kasar take dauka, sun wuce babban gargadi kawai ga masu hura wutar rikici ga kasar Sin, domin kuwa hakan ya zama kokari na kiyaye mulkin kai da cikakkun yankunan kasa, kuma martani ne ga Amurka, don taimakawa kasashe da yankunan da suka ji radadi, daga “demokuradiyya mai salon Amurka”. (Murtala Zhang)