logo

HAUSA

Rundunar PLA dake gabashi na ci gaba da atisayen hadin gwiwa don gwada dabarunta na kai hari

2022-08-08 11:10:09 CMG Hausa

Rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ta PLA, ta ci gaba da yin atisayen hadin gwiwa ta ruwa da kuma sararin samaniyar tsibirin Taiwan kamar yadda aka tsara.

Atisayen na jiya, ya mayar da hankali ne kan gwada karfin kai farmaki na hadin gwiwa, kan wuraren da aka tsara ta kasa da kuma kai hare-hare ta sama.

Rundunar sojin sama karkashin rundunar dake gabashi, ta tura jiragen yaki iri-iri da suka hada da jiragen aikewa da gargadi na farko, da jiragen jefa bama-bamai, da jiragen yaki, domin gudanar da atisaye, kamar leken asiri na hadin gwiwa, da aikin kula da sararin samaniya, da kai hare-hare ta kasa kan wuraren da aka tsara, da bayar da kariya ta sama da kaucewa abokan gaba. (Ibrahim Yaya)