logo

HAUSA

Mutane 24 sun rasu wasu 215 sun jikkata yayin dauki ba dadin dakarun Isra’ila da Falasdinu

2022-08-07 17:00:46 CMG Hausa

Yayin da aka shiga yini na 2, da fara dauki ba dadi tsakanin dakarun Isra’ila da na Falasdinu, a kalla falasdinawa 24 sun rasu, an kuma jikkata karin wasu 215.

Rahotanni na cewa, sojojin Isra’ila da dakarun kungiyar jihadi ta falasdinawa ko PIJ, sun ci gaba da kaiwa juna hare hare, kuma cikin wadanda suka rasu a bangaren falasdinawa har da yara kanana 6 da mata 2.

A daren jiya Asabar, sojin saman Isra’ila sun kaddamar da hari a garin Rafah, na kudancin zirin Gaza ba tare da wani gargadi ba, harin da ya hallaka falasdinawa 2, tare da jikkata mutane sama da 30.

Cikin wata sanarwa, kakakin sojin Isra’ila Avichai Adraee, ya ce sun hari gidan Khaled Mansour, kwamandan rundunar PIJ yankin kudanci. To sai dai PIJ ba ta tabbatar da rasuwan Mansour ba, sai dai kungiyar ta ce harin ya hallaka Ziad Al Mudallal, daya daga mambobin ta.

A wani ci gaban kuma, wata majiyar tsagin falasdinu ta ce a kalla yara 4 da wani mutum guda sun rasu, wasu kuma 15 sun jikkata a harin daren ranar Asabar, lokacin da wani makami ya fashe, a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza.

Isra’ila dai ta musanta hannu cikin aukuwar fashewar, tana mai cewa, wani makamin roka da PIJn ta harba ne ya kuskure, ya fada kan sansanin na ‘yan gudun hijira mai kunshe da yara kanana. (Saminu)