logo

HAUSA

Fitaccen mai zane na kasar Sin Chen Jialing

2022-08-06 18:12:31 CMG Hausa

Yayin taron kungiyar G20 na 2016, akwai wani babban hoto da ake kira da “Scenery of West Lake” wanda ya zama shimfidar dake bayan hoton da shugabannin kasashen duniya suka dauka tare. Hoton mai tsawon mita 2, ya taimakawa mutane a fadin duniya jinjinawa kyawun fasahar zanen fenti na zamani, na kasar Sin. Wanda ya zana wannan hoto shi ne Chen Jialing.

Cikin shekaru da dama, Chen Jianling ya yi fice cikin masu fasahar zane a kasar Sin a matsayin mai burin kawo sauyi. Bayan fara zanen fenti na gargajiya na kasar Sin, ya jajirce wajen kirkirowa tare da gwada sabbin abubuwa a rukunoni daban-daban kamar zanen mutane da wurare da furanni da tsuntsaye.