logo

HAUSA

Kasar Sin ta soki Amurka bisa yadda ayyukanta ke sabawa burin kwance damarar makamai

2022-08-06 19:03:01 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin kan harkokin da suka shafi kwance damarar makamai, Li Song, ya caccaki Amurka, game da matakanta da suka sabawa burin kwance damarar makamai.

Li Song, ya shaidawa taron kwamiti kan nazari karo na 10 na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya NPT cewa, Amurka na amfani da yakin cacar baka wajen neman iko da fifiko da yin takara, har ma da karfafa kawance soji da haddasa fito na fito a yankunan gabashi da yammacin Turai da Asia. Haka kuma ta yi gaban kanta wajen girke makaman nukiliya da dakaru, da kawo tsaiko ga daidaito da zaman lafiyar duniya, tare da barazana ga kokarin duniya na kawar da makaman nukilya, da kuma kara barazanar yaduwar makaman da rikice-rikice.

A cewarsa, ya kamata kasashen duniya su yi amfani da wannan taro wajen kiyaye tsarin huldar kasa da kasa bisa gaskiya, da adawa da yakin cacar baka da kishi, da daukaka burinsu na bai daya na hadin kai da samun tsaro mai dorewa a duniya, tare da tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin da suka dace na inganta tsarin kwance damarar makaman nukiliya a duniya da kuma inganta karfi da ikon yarjejeniyar NPT. (Fa’iza Mustapha)