logo

HAUSA

Sin da ASEAN sun yaba nasarorin da aka cimma a karkashin kyakkyawar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu

2022-08-05 11:27:53 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da na Asean, inda bangarorin biyu suka bayyana irin nasarorin da aka cimma a hadin gwiwarsu, tare da yin alkawarin gina al'ummar Sin da ASEAN mafi kusa mai makoma ta bai daya.

Taron da ya gudana jiya Alhamis, wanda Wang Yi da mataimakin firaministan kasar Cambodia, kana ministan harkokin wajen kasar Prak Sokhonn suka jagoranta, ya samu halartar ministocin harkokin wajen kasashe 10 na kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, da babban sakataren kungiyar Dato Lim Jock Hoi.

Wang Yi ya kuma gana da takwaransa na kasar Turkiye Mevlut Cavusoglu ranar Laraba a gefen taron ministocin harkokin waje kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen gabashin Asiya, inda ya sha alwashin inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa jawabin Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tilo a duniya, ba wai kan batun Taiwan kadai ba, har ma da batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang. Yana mai cewa, bangaren Turkiye ya yi farin ciki kan ziyarar da shugabar hukumar kare hakkin bil-adama ta MDD Michelle Bachelet ta kai jihar Xinjiang. Ya ce, yana fatan ci gaba da tuntubar kasar Sin game da batutuwan da suka shafi ziyarar da tawagar kasar Turkiye za ta kai jihar Xinjiang.

Cavusoglu ya ce, kasarsa tana martaba cudanyar bangaori daban-daban, da nuna adawa da kakkaba takunkumai na kashin kai. Yana mai cewa, Turkiye na son karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, don tinkarar matsalar samar da abinci, da sauran al’amura masu wuyar gaske, sakamakon manyan kalubalen da rikicin Ukraine ya haifarwa farfadowar tattalin arzikin duniya. (Ibrahim Yaya)