logo

HAUSA

Kakakin jami’an diplomasiyar Sin dake kungiyar EU: Sinawa biliyan 1.4 ne za su yanke hukunci kan batun Taiwan

2022-08-04 17:27:52 CMG Hausa

A jiya ne, ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da babban wakilin EU mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro, suka ba da sanarwa cewa, matakin da kasar Sin ta dauka game da ziyarar Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan, na iya haifar da tashin hankali da rashin zaman lafiya a yankin, inda suka yi kira ga bangaren Sin, da kada canja halin da ake ciki yanzu ta hanyar amfani da karfin tuwo, a maimakon haka a warware sabani cikin lumana.

Game da wannan batu, kakakin tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar kasashen Turai EU ya nuna cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, kuma tsoma baki a cikin harkokin yankin cin zarafi ne ga ikon mulkin kasar Sin. “Bisa ka’idojin kasa da kasa” dake cikin sanarwar da ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 da na EU suka bayar, ya kasance kamar yadda wasu ’yan fashi suka buga wani, wani bai iya mayar da martani ba.

Yanayin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan ya canza ya shiga cikin mawuyacin hali, wa ya kawo wa barazana? Kuma wa ya tsokaci wani? An kawo babbar barazana ga cikakkun yankunan kasar Sin, har ma ikon mulkin kasar. Don haka ya zama wajibi da dacewa da gwamnatin Sin ta dauki matakan kare ikon mulkin kasa da cikakkun yankunanta. Shi ne babban buri na daukacin al’ummun Sinawa biliyan 1.4 gaba daya. (Safiyah Ma)