logo

HAUSA

Mahukuntan Taiwan na tsunduma Taiwan cikin mawuyacin hali

2022-08-03 14:02:54 CMG Hausa

Kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Ma Xiaoguang ya bayyana a yau Laraba cewa, Cai Yingwen da ma jam’iyyar DPP sun dade da tsayawa kan matsayinsu na neman ’yancin kan Taiwan, tare da kin amincewa da daidaiton da aka cimma a shekarar 1992, har ma sun hada kai da wasu kasashen waje, inda suka kare aniyar gayyatar Nancy Pelosi ta kai ziyara yankin Taiwan, don neman ballewar yankin, ba tare da yin la’akari da zaman lafiyar yankin zirin Taiwan da ma tsaron al’ummar yankin ba.

Ma Xiaoguang ya kuma yi gargadin cewa, yadda Cai Yingwen da jam’iyyar DPP ke hada kan wasu kasashe don neman ballewar yankin Taiwan, neman cimma moriyar jam’iyya suke yi, sai dai hakan zai kara saurin dakile su, tare da tsunduma Taiwan cikin mawuyacin hali.

Har wa yau, Ma Xiaoguang ya ce, babban yankin kasar Sin ya yanke shawarar daukar matakan hukunci a kan hukumomin ’yan aware na Taiwan masu taurin kai, wadanda suke fakewa da sunan “dimokuradiyya” da “hadin gwiwar neman ci gaba” wajen gudanar da aikace-aikacen neman ballewar yankin daga kasar Sin. (Lubabatu Lei)