logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Ga Yadda Nancy Pelosi Ta Je Yankin Taiwan Na Kasar

2022-08-03 00:08:48 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, yadda shugabar majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta rufe kunnenta game da kin amincewar da bangaren kasar Sin ta nuna, inda ta tafi ziyara a yankin Taiwan na kasar, ya sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da bayanan hadaddun sanarwoyi guda 3 da kasashen Sin da Amurka suka gabatar a baya, lamarin da ya girgiza tushen alakar Sin da Amurka, da keta ikon kasar Sin na mulkin kai da na kare cikakken yankin kasa. Saboda haka kasar Sin ta yi Allah wadai da lamarin da babbar murya, tare da nuna matukar rashin jin dadi ga bangaren kasar Amurka.

A sa’i daya, rundunar sojojin kasar Sin ta PLA ta sanar da shirin kaddamar da atisayen soja a wasu yankunan dake dab da yankin Taiwan na kasar, tsakanin ranar 4 zuwa ranar 7 ga watan nan na Agusta.

Kakakin zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da kwamiti mai kula da harkar hulda da kasashen waje na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar, da ofishin kula da ayyuka masu alaka da yankin Taiwan na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, dukkansu sun bayyana takaici da kin amincewa game da tafiyar Nancy Pelosi zuwa yankin Taiwan na kasar Sin. (Bello Wang/Jamila Zhou)