logo

HAUSA

Hua Chunying: Amurka za ta girbi sakamakon keta hurumin ‘yancin mulkin kai da tsaron kasar Sin

2022-08-02 19:19:13 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Amurka na daukar wasu miyagun matakai, da ka iya rura wutar rashin jituwa a zirin Taiwan, kuma alhakin abun da zai biyo baya zai rataya a wuyan ta.

Hua Chunying, wadda ta bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce ko shakka babu, Amurka za ta girbi sakamakon keta hurumin ‘yancin mulkin kai, da tsaron kasar Sin.  (Saminu Alhassan)