logo

HAUSA

Bankin duniya ya amince da shirin tattara kudi domin saukaka matsalar hatsi a kasashe uku dake yammacin Afirka

2022-07-31 15:58:32 CMG Hausa

Bankin duniya ya amince da wani shirin tattara kudi domin saukaka matsalar karancin hatsi da kasashe uku wato Chadi da Ghana da Saliyo dake yammancin Afirka suke fuskantar.

Bisa shirin wanda aka zartas a ranar 29 ga wata, kungiyar raya kasa da kasa, za ta tattara kudin da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 315, domin taimakwa karin mutane miliyan 2 wadanda ke fama da matsalar karancin abinci a wadancan kasashe uku.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, mutane kusan miliyan 38.30 dake rayuwa a yammacin Afirka, za su yi fama da matsalar karancin abinci. (Jamila)