logo

HAUSA

Daruruwan mutanen Afrika na adawa da hana musu visar halartar taron duniya kan cutar Kanjamau da Canada ta yi

2022-07-31 16:24:53 CMG Hausa

An bude taron duniya kan cutar kanjamau ta AIDS a birnin Montreal na Canada. Taron da aka bude a jiya Asabar, shi ne irinsa mafi girma kan cutar a duniya, haka kuma muhimmin dandali ne na yayata matakan kariya da magance cutar. Masana kimiyya da masu fafutuka daga fadin duniya, su kan yi amfani da wannan gagarumar dama, wajen tattauna batutuwan da suka shafi yaki da cutar ta kanjamau. Sai dai a bana, daruruwan mahalarta daga Afrika ba su samu damar halarra ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu manufofin wariya wajen bada visa na gwamnatin kasar Canada.

Wata mai fafutukar yaki da cutar a Afrika ta Kudu, Viiseka Dubra, ta ce wannan taron na su ne, wato masu ruwa da tsaki kan yaki da cutar kanjamau, yana mai cewa, dole ne su yi magana saboda an hana su shiga kasar. Kana bai kamata a rika gudanar da taro a kasar dake nuna wariyar launin fata ba.

Masu zanga-zanga sun bayyana adawa da matakin gwamnatin Canada na hana damar shiga kasar ga daruruwan mahalarta taron, galibinsu daga Afrika, saboda rashin daidaiton da ya kai ga karuwar yaduwar cutar. Sun bayyana cewa, ya kamata tarukan duniya kan yaki da cutar kanjamau, su tabbatar da ana damawa da kwararru daga yankunan da suka fi fama da cutar.

Gwamnatin Canada dai bata bayyana dalilanta na hana visar shiga kasar ba, amma wasu daga cikin wadanda ta hanawa visar, sun ce kasar bata yarda cewa za su tafi bayan an kammala taron ba. (Fa’iza Mustapha)