logo

HAUSA

Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Gaggauta Daidaitawa Da Ma Dage Takunkuman Da Aka Kakabawa Kasashen Afirka Da Ba Su Biya Bukatun Halin Da Ake Ciki Ba

2022-07-30 16:02:41 CMG Hausa

Jiya ne, kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro, inda ya zartas da kuduri mai lamba 2588 kan takunkuman da aka kakabawa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda kasar Faransa ta gabatar, ya kuma samu kuri'u 10 na goyon baya da kuma 5 na kauracewa kada kuri'a.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya halarci taron, inda ya kaurace wa kada kuri'a, kana ya yi bayani kan matsayin kasar Sin na kauracewa kada kuri’ar.

Dai Bing ya ce, kasar Sin na maraba da kudurin, wanda ya daidaita matakan takunkuman hana shigo da makamai da aka sanyawa gwamnatin Afirka ta Tsakiya.

A hannu guda kuma, kasar Sin ta yi imanin cewa, kudurin yana da wasu matakai na takaita zirga-zirga, wadanda za su iya kawo tsaiko ga kokarin da gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya ke yi, na kara karfin tsaron kasar. Kuma har yanzu akwai dama ta ingantawa, har sai an dage takunkuman baki daya.

Dai ya jaddada cewa, ya kamata mambobin kwamitin sulhun da abin ya shafa, su mai da hankali kan batutuwa masu ma'ana gami da bukatun kasashen Afirka, da gaggauta daukar matakai bisa gyare-gyaren takunkuman hana shigo da makamai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tare da yin nazari sosai kan batutuwan dake kunshi cikin takunkuman da aka kakabawa kasashen Afirka, da daidaitawa a kan lokaci da ma soke matakan takunkuman da ba su dace da bukatun halin da ake ciki ba. (Ibrahim)