logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Bukatar Sinawa A Gida Da Waje Da Su Hada Karfi Da Karfe Domin Samun Farfadowa

2022-07-30 20:28:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar al’ummar Sinawa a cikin gida da wajen kasar, da su hada kai tare da yin aiki tukuru, don kara karfi, don farfado da al’ummar Sinawa.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin koli na sojojin kasar, ya bayyana haka ne a yayin wani taron koli na aikin hadin gwiwa da aka gudanar daga jiya Juma'a zuwa Asabar din nan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.(Ibrahim)