logo

HAUSA

Ma’aikatar tsaron kasa ta Sin ta mayar da martani ga “Dokar izinin tsaro ta kasa ta 2023” ta Amurka

2022-07-29 16:31:02 CMG Hausa

A jiya Alhamis, shugaban ofishin watsa labarai na ma’aikatar tsaron kasar Sin, kuma kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya mayar da martani kan abubuwan da suka shafi kasar Sin dake cikin “Dokar izinin tsaro ta kasa ta 2023” ta Amurka, cewa yana da matukar hadari ga Amurka ta yi wasa da wuta ta hanyar fadin wani abu da yin wani na daban, wanda ya kawo babbar illa ga dangantaka tsakanin sojojin Sin da na Amurka, da yadda hakan ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin mashigin tekun Taiwan, kuma yi matukar habaka hadarin fito-na-fito na sojojin Sin da Amurka.

Wani ya yi tambayar cewa, “Dokar izinin tsaro ta kasa ta 2023”, wadda majalisar wakilan Amurka ta zartar ta sake bayyana “taimakon Amurka ga tsaron yankin Taiwan”, inda aka nuna cewa, sojojin Amurka suna da ikon gudanar da atisayen soja na hadin kai tare da Taiwan, da kuma gayyatar Taiwan shiga cikin “atisayen soja dake kewayen tekun Pasific” da dai sauransu, kana gwamnatin Amurka ta zartar da sabon karon sayar da makamai ga yankin Taiwan, shin ko mene ne ra’ayin bangaren Sin game da wannan?

Wu Qian ya ce, yankin Taiwan daya ne daga sassan kasar Sin, kuma harkokin yankin Taiwan harkoki ne na cikin gidan Sin, don haka bai dace bangaren Amurka ya sa baki a ciki ba. A hannu daya, bangaren Amurka ya yi da’awar cewa, yana bin manufar kasar Sin daya tak, kuma ba ya nuna goyon baya ga ‘yancin kai na yankin Taiwan, a daya bangaren kuma ya karfafa hadin gwiwar sojoji, da siyasa tsakaninsa da yankin Taiwan na Sin, ya kuma fitar da shirin sayar da makamai ga yankin Taiwan, ko shakka babu wannan irin danyen aiki na yin wasa da wuta yana da matukar hadari. (Safiyah Ma)