logo

HAUSA

Amurka Ta Kau Da Kai Daga Aikin Tilas Da Fataucin Mutane Cikin Daruruwan Shekaru!

2022-07-29 20:35:24 CMG Hausa

Kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gabatar da rahoton shekara-shekara dangane da aikin tilas da fataucin mutane, inda ta soki kasashen duniya, tare da ayyana kanta a matsayin mai kiyaye hakkin dan Adam.

Duk da abun da aka wallafa a shafin internet na ma’aikatar aiwatar da doka ta Amurka a watan Nuwamban bara, ta nuna ainihin gaskiyar Amurka. An yaudari ‘yan kwadago fiye da 100 daga kasar Mexico da sauran kasashen nahiyar Amurka ta tsakiya zuwa kudancin jihar Georgia ta Amurka don yin aikin tilas. Sun yi girbin albasa da hannu cikin tsananin rana, yayin da masu dauke da makamai suke sa musu ido. Inda ake ba su senti 20 kawai a ko wane bokiti na albasa. Da dare kuma, su kan kwanta ne a cikin rumfa mai cunkuson mutane kuma maras tsabta. Ba su da isasshen abinci da ruwa mai tsabta. Mutane a kalla 2 sun rasa rayukansu a cikin wannan hali maras kyau, kamar yadda aka tilastawa ‘yan asalin Afirka zama bayi yau shekaru fiye da 200 da suka wuce.

Masharhanta sun yi nuni da cewa, Amurka da ke kiran kanta mai rajin kare hakkokin bil Adama, ta yi cinikin bayi a baya, kuma yanzu tana fataucin mutane da sanya aikin tilas. Amurka tana gudanar da ciniki na rashin tausayi da zubar da jini cikin duhu ba tare da wani tausayi ba. (Tasallah Yuan)