logo

HAUSA

Wang Yi: Ya Dace A Ci Gaba Da Ruhun Shanghai Da Gina Al'ummar SCO Mafi Kusanci Mai Makomar Bai Daya

2022-07-29 20:54:11 CMG Hausa

Yau ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a Tashkent, babban birnin Uzbekistan.

Wang Yi ya bayyana cewa, a yau duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauye-sauye. Kuma sauye-sauyen da ba a taba gani ba cikin karni, suna da nasaba da yanayin annobar wannan karni, kana batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya na ci gaba da tabarbarewa.

Ya kara da cewa, bunkasuwa da zaman lafiya, ayyuka ne masu wahalar gaske ga dukkan kasashe. Don haka ya ce, akwai bukatar a ci gaba da ruhun Shanghai, da yin aiki tare da taimakon juna domin gina al'ummar SCO mafi kusanci mai makomar bai daya.

Wang Yi ya kuma gabatar da shawarwarin kasar Sin kan wannan batu: na farko, karfafa hadin kai da taimakon juna. Na biyu, karfafa tsaron yankin. Na uku, inganta ci gaba mai dorewa. Na hudu, kiyaye hadin gwiwar bangarori daban-daban. Sai na biyar kuma na karshe, inganta ci gaban kungiyar.(Ibrahim)